Matthew 26

An Ƙulla Shawara Gāba da Yesu

1Saʼad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa, 2“Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu-za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”

3Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist da ake kira Kayifas, 4suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi. 5Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, in ba haka ba mai yiwuwa a yi hargitsi.”

An Shafe Yesu a Betani

6Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, 7wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.

8Saʼad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! 9Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”

10Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne. 11Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba. 12Saʼad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don janaʼizata. 13Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi waʼazin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

Yahuda Ya Yarda Yǎ Bashe Yesu

14Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan-wanda ake kira Yahuda Iskariyot-ya je wurin manyan firistoci 15ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. 16Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.

Abincin Yamma na Ubangiji

17A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya, “Ina kake so mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”

18Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka’ ” 19Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.

20Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun. 21Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 22Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Ubangiji?”

23Yesu ya amsa, ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni. 24Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”

25Saʼan nan Yahuda, wanda zai bashe shi, ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?”

Yesu ya amsa, ya ce, “I, kai ne.”
Ko kuwa “Kai kanka ka fada”


26Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”

27Saʼan nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai. 29Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”

30Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.

Yesu Ya Yi Maganar Mūsun da Bitrus zai Yi

31Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya sabili da ni, gama a rubuce yake cewa:

“ ‘Zan bugi makiyayin,
tumakin garken kuwa za su fasu.’
Zak 13.7

32Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”

33Bitrus ya amsa, ya ce, “Ko da duka sun ja da baya sabili da kai, ba zan taɓa ja da baya ba.” 34Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”

35Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.

Getsemane

36Saʼan nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi adduʼa.” 37Ya ɗauki Bitrus da ʼyaʼya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu. 38Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”

39Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi adduʼa, ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”

40Saʼan nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus, ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na saʼa guda ba? 41Ku yi tsaro, ku kuma yi adduʼa, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

42Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi adduʼa, ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”

43Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci. 44Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi adduʼa sau na uku, yana maimaita iri abu guda.

45Saʼan nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, saʼa ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi. 46Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”

An Kama Yesu

47Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su. 48To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su: “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.” 49Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Saʼan nan ya yi masa sumba.

50Yesu ya amsa, ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.”
Ko kuwa “Aboki, me ya kawo ka?”


Saʼan nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.
51Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.

52Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu. 53Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yǎ aiko mini fiye da rundunar malaʼiku goma sha biyu ba? 54Amma ta yaya za a cika Nassin da ya ce dole haka yǎ faru?”

55A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagorar wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna don ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba. 56Amma wannan duka ya faru ne don a cika rubuce rubucen annabawa.” Saʼan nan dukan almajiran suka yashe shi suka gudu.

A gaban Majalisa

57Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru. 58Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yǎ ga ƙarshen abin.

59Sai manyan firistoci da ʼyan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi. 60Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito.

A ƙarshe, biyu suka zo gaba,
61suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”

62Saʼan nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?” 63Amma Yesu ya yi shiru.

Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai: Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”

64Sai Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka: Nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”

65Saʼan nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon. 66Me kuka gani?”

Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”

67Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi 68suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”

Bitrus Ya Yi Mūsun Sanin Yesu

69To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu Bagalile.”

70Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”

71Saʼan nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”

72Ya sāke mūsu har da rantsuwa: yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”

73Bayan ɗan lokaci, sai na tattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”

74Sai ya fara laʼantar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!”

Nan da take, sai zakara ya yi cara.
75Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.

Copyright information for HauSRK